Paparoma Francis zai jagoranci adu'ar bikin Easter

Paparoma Francis
Image caption Paparoma Francis

Nan bada jimawa ba Paparoma Francis zai gudanar da bukin Easter wacce itace ranar data fi kowace tsarki ga mabiya addinin kirista, inda zai jagoranci addu'o'i a dandalin Saint Peters da safiyar yau.

Bukin zai hada da sakonsa na farko da ake kira 'Urbi et Orbi' ga mutane dake birnin dama duniya baki daya a matsayinsa na sabon Paparoma.

Shi dai Paparoma Francis zai gabatar da jawabin nasa ne a baranda da ya fara fitowa a lokacin da aka zabe shi makonni uku da suka gabata.

Wakilin BBC a Rome ya ce dubban mabiya ne daga kasashen duniya suka hallara a birnin Rome don halarta bukukuwan Easter da za'a gudanar yau lahadi inda a za'a yi addu'o'i a dandalin Saint Peters.