An kashe dan sanda a garin Kumo na Gombe

ig
Image caption Speto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar

Rahotanni daga garin Kumo da ke jihar Gombe a arewacin Najeriya na cewa, an shafe daren jiya (ranar Juma'a) ana jin karar harbe-harbe a garin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Muhammadu Sule ya shaida wa BBC cewa, wasu 'yan bindiga da ya kira bata gari ne ake zargin sun kai hari gidan wani dan sanda da ke garin inda suka bindige shi.

Wadanda suka kai harin sun kuma kashe wani da aka ce malamin addinin kirista ne a garin.

Sai dai kwamishinan 'yan sandan ya ce sun kama mutane biyu daga cikin wadanda suka kai harin, tare da kwace bindigogi biyu kirar AK 47 da kuma baburan hawa biyu.

Karin bayani