Zabe: Kotun kolin Kenya za ta bayyana hukunci

Image caption Pira Minista Raila Odinga ya kalubalanci zaben da ya baiwa Uhuru Kenyatta nasara

A yau ne Kotun Kolin Kenya za ta bayyana hukuncin da ta yanke a kan sahihancin zaben shugaban kasar da aka gudanar a wannan watan.

Piraminista Raila Odinga dai bai amince da zaben ba, bayan da Uhuru Kenyatta ya samu nasara akan sa.

Mr.Odinga dai na zargin cewa an samu kura-kurai da kuma matsalar na'ura a yayin zaben, hakan ya sa kotun ta bada umarnin sake kirga kuri'un cibiyoyin zabe guda ashirin da biyu.

Ranar tara ga watan na Maris ne dai aka bayyana Uhuru Kenyatta, dan shugaban kasar ta Kenya na farko bayan samun mulkin kai, a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Shugaban kasar mai barin gado, Mwai kibaki ya yi kira ga dukkanin bangarorin da su amince da hukuncin da kotun zata yanke.