Shugaban Kenya ya yi alkawarin aiki tare da kowa

kenayyta
Image caption Uhuru Kenyatta tare da magoya bayansa

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta wanda kotun Kolin kasar ta tabbatar da nasarar zabensa a matsayin shugaban kasar, ya yi alkawarin aiki tare da dukkanin 'yan kasar ba tare da nuna banbanci ga wani bangare ba.

Ha kuma abokin hammayasa Firayminista Raila Odinga ya amince da hukuncin kotun koli kuma ya ce be kamata yan kasar su bar zaben ya kawo rarabuwa kawuna tsakaninsu ba

Shi kuwa a nasa bangaren Mr Uhuru Kenyatta ya kira tsohon abokin hammayasa dan uwansa kuma ya nemi shi a kan su yi aiki tare da sabuwar gwamnati.

Sai dai kungiyar agaji ta Red cross ta shaidawa BBC cewa mutane biyu sun hallaka yayinda goma sha daya sun ji raunuka a tashin hankalin da ya barke a garin Kisumu a yammacin kasar sakamakon hukuncin da kotun kolin a lokacinda magoyan bayan Mr Raila Odinga suka yi artabu da yan sanda .

A jiya ne dai kotun kolin kasar ta tabbatar da Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a farkon wannan watan.

Mista Uhuru Kenyatta dane ga shugaban Kenya na farko.

Karin bayani