Koriya ta arewa na barazana ga Koriya ta kudu

Image caption Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un na shirye-shirye da kwamandojin sojin kasar

Koriya ta arewa ta ce tana yanayin yaki ne a yanzu haka da Koriya ta kudu.

Kasashen biyu dai suna yanayin yaki ne tun da aka yi yakin koriya, shekaru 60 da su ka wuce inda aka cimma yarjejeniyar tsagaita a wuta ba, ba na zaman lafiya ba.

Amma furucin da ya fito daga Pyongyang yanzu dai ya zo ne a lokacin da ake zaman dar-dar a yankin na Koriya.

Wata sanarwa da gwamnatin Koriya ta arewa ta fitar wadda aka yadda a kafar yadda labaran gwamnatin kasar ta ce daga yanzu kasar za ta rika mu'ala ne da Koriya ta kudu kamar ana wani yanayi na yaki.

Ta ce idan har Koriya ta kudu ta tunzura ta za ta yi yaki da ita tare da amfani da makaman nukuliya.

Kasashen biyu dai na cikin wani yanayi ne na yaki na kusan shekaru sittin kenan, tunda har yanzu ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba, tsakaninsu.

Duk da cewa dai kasashen biyu basu bayyana hakan ba, amma furucin na Pyongyang ya tabbatar da haka. Wannan dai na kara fito da irin halin rashin tabbas din da ake da shi a Koriya.

Tuni dai koriya ta arewa ta janye daga yarjejeniyar Armistice da ta raba iyakar soji tsakaninta da kudu.

Masu hasashe da dama na ganin kokari yaki da Koriya ta kudu da kuma Amurka da gwamnatin Koriya ta arewa ke kokarin yi zai zama babban koma baya gare ta.

Karin bayani