Mandela ya soma murmurewa

Nelson Mandela
Image caption Nelson Mandela

Za a dai yi wa Nelson Mandela adu'o'i a coci-coci a sasa daban-daban a kasar Afrika ta Kudu yayinda ake bikin Easter.

Ana sa ran daruruwan mutane za su halara da safiyar yau a cocin Regina Mundi a birnin Soweto. Cocin a baya ya kasance wurin da masu fafitukar kawarda wariyar launin fata ke taruwa domin su tattauna.

A daren larabar da ta gabata ne aka kwantar da Nelson Mandela a asibiti bayan fadar shugaban kasa ta bayana cewa ya sake kamuwa da cutar pneumonia.

Ta kuma kara da cewa majina ta taru masa sakamakon cutar huhun da yake fama da ita, ko da yake fadar shugaban kasa ta ce ya fara murmurewa sakamakon kulawar da yake samu.

Kakakin shugaban kasa , Mac Maharaj, wanda ya taba zaman gidan kurkuku tare da Mr Mandela a tsibirin Robben a shekarun 1960 da kuma 1970 ya yi godiya ga mutanen da suka rika yi wa tsohon shugaban kasar adu'a da kuma sakonin fatan alheri da suka rika turo masa.

Wannan dai shi ne karo na uku da Mr Mandela zai kasance a asibiti tun bayan watan disembar bara kuma ba'a sake ganinsa a cikin bainar jama'a ba tun bayan gasar kofin kwallon kafa ta FIFA da aka yi a kasar kusan shekaru uku da suka gabata.