An kashe mutane 15 a wani samame a Kano

boko haram
Image caption 'Yan boko haram na kai hare-hare sosai a Najeriya

Rahotanni daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya na cewa akkala mutane goma sha biyar ne suka rasa rayukansu a wani samame da sojoji suka kai yankin Unguwa uku da ke birnin.

Jami'an tsaron sun ce sun kai samamen ne kan wani gida da suke zargin maboyar 'yan kungiyar nan ne ta Jama'atu Ahlussunnah Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram.

Wani jami'in tsaro, Iliyasu Abba ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar " an kai samame ne sakamakon bayannan sirri da suka samu".

Mazauna yankin na unguwa uku da kewaye dai sun ce sun wayi garin yau ne da jin karar harbe harbe da kuma fashewar abubuwa.

Karin bayani