Ana bata kashi a Timbuktu na Mali

mali
Image caption Sojojin Mali sun fatattaki 'yan tawaye

Dakarun kasar Mali da jiragen yakin Faransa sun cigaba da bata kashi tsakaninsu da 'yan tawaye a Timbuktu na arewacin Mali.

Hakan ya biyo bayan matakin da wani dan kunar bakin wake ya kashe kansa dafda shingen binciken da sojoji suka kafa.

Kakakin dakarun Malin, Modibbo Naman Traore ya ce dan kunar bakin wake ya yi amfani ne da motar ce, don ya dauke hankalin jam'ian tsaro, don baiwa 'yan tawaye damar shiga garin cikin dare.

Ya kara da cewar har yanzu ana cigaba da musayar wuta a birnin Timbuktun.

Karin bayani