Gubar darma ta kashe yara 450 a jihar Zamfara ta Najeriya

Aikin kwashe a kasa mai guba a jihar Zamfara
Image caption Aikin kwashe a kasa mai guba a jihar Zamfara

Kungiyar bayar da agajin likitoci ta MSF, ta zargi gwamnatin Najeriya da jan kada da kuma mayar da martani marar inganci game da gurbatar kauyuka a jihar Zamfara dake arewacin kasar da gubar darma.

Yara fiye da 450 ne suka mutu sakamakon gubar darma a cikin shekaru 4, sannan ana yiwa wasu dubbai magani.

Mutanen kauyukan na yin amfani da dalmar mai tsananin guba ne domin samun taimakon hako zinari, wanda sakamakon haka yake gurbata kasar dake zagayen gidajensu.

Kungiyar bayar da agajin likitocin ta MSF ta nemi sanin abinda ya sa gwamnati ba ta aike da masana ilmin kimiya da likitoci domin taimakawa ga magance matsalar ba.

Gwamnatin dai ta ce tana yin iya abinda za ta iya yi, sannan ta zargi mutanen kauyen da hakar ma'adinai ba bisa doka ba.

Karin bayani