Japan ta bayyana shirin kara yawan kudaden da kasar ke bugawa

Shugaban Babban Bankin Japan
Image caption Shugaban Babban Bankin Japan

Sabon Gwamnan Babban Bankin Japan, ya bada sanarwar wasu sababbin shirye-shirye na kara yawan kudaden da kasar ke bugawa a wani yunkuri na magance matsalar faduwar farashin kayyaki da aka shafe shekaru fiye da 10 ana fama da ita a kasar.

Haruhiko Kuroda, wanda ya hau kan mukaminsa a watan jiya, yana so ne farashin kayyaki ya hau zuwa kashi 2 cikin 100 nan da shekaru 2 masu zuwa.

Wakilin BBC ya ce masana harkokin tattalin arziki, sun yi amannar cewa yadda farashin kayyaki ya rika faduwa a Japan a cikin shekaru 15 da suka wuce, ya sa 'yan kasar suna dari-dari wajen sayen kayyaki, sannan kuma kamfanonin kasar ba sa son zuba jari, abun da ke kawo kawo cikas wajen cigaban tattalin arzikin kasar.