Ruwan sama ya rusa gidaje a jihar Pilato

Gidajen da suka ruguje sakamakon ruwan sama a ihar Pilato
Image caption Gidajen da suka ruguje sakamakon ruwan sama a ihar Pilato

Gidaje da makarantu da sauran wurare fiye da dari daya ne suka salwanta a garin Jingir na Jihar Pilaton Najeriya.

Lamarin ya faru ne sakamakon wani ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya a yankin.

Garuruwa da birane da yawa ne dai kan fuskanci matsalolin ruwan sama da iska da kuma ambaliyar truwa a Najeriya sakamakon rashin kyawawan magudanan ruwa da kuma rashin ingantaccen tsarin garuruwa.