Koriya ta arewa ta gargadi baki da ke Kudu

Shirin sojin Koriya ta Arewa
Image caption Shirin sojin Koriya ta Arewa

Korea ta arewa ta shawarci kamfanonin kasashen waje da kungiyoyi da yan yawon bude idanu dake cikin Koriya ta Kudu su fara duba yiwuwar barin kasar domin kare rayuwarsu.

Kafar yada labaran gwamnatin Koriya ta arewa ta ruwaito mahukuntan kasar na cewa basa fatan ganin yaki ya ritsa da yan kasashen wajen.

Wata mai karanta labarai a gidan talabijin din kasar ta bada wannan sanarwa.

" Ta ce Koriya ta arewa bata son ganin baki yan kasashen waje a cikin Koriya ta kudu sun fada tarkon rikicin yakin. Gwamanati na fadakar da dukkan hukumomi na kasashen waje da cibiyoyin kasuwanci da yan yawon bude idanu a birnin Seoul da sauran wurare a cikin Koriya ta kudu da su dauki matakin kauracewa tun wuri domin kariyar kansu."

A halin da ake ciki kuma kasar Japan tace ta girke naurori masu kakkabo makamai masu linzami a daura da tsakiyar birnin Tokyo za kuma ta yi amfani da su wajen harbo dukan wani makami mai linzami da ya ratsa ta sararin samaniyar kasar.