Shugaban masu kishin Islama na Syria ya nuna biyayya ga Al-Zawahiri

Kungiyar Alnasr mai nasaba da al-qa'ida a Syria

Wani jagoran kungiyar adawa a Siriya da ake kira Nusra Front mai tsananin kishin Islama ya baiyana mubaya'a ga Ayman Zawahiri wanda ya gaji Osama bin Laden a matsayin shugaban kungiyar al-Qa'ida.

Sai dai kuma Abu Mohammad al-Joulani ya nesanta kungiyarsa daga sanarwar da kungiyar al-Qaida a Iraqi ta bayar cewa kungiyoyin biyu za su hade.

A wani sako mai dauke da sautin murya da aka sanya a shafin Internet, shugaban kungiyar Nusra yace ba'a tuntube shi a game da shirin hadewar kungiyoyin biyu ba.