Majalisar Dinkin Duniya ta amince da yarjejeniyar takaita cinikin makamai

Yarjejeniyar takaita makamai ta majalisar dinkin duniya
Image caption Yarjejeniyar takaita makamai ta majalisar dinkin duniya

Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarumin rinjaye yarjejeniyar farko ta kasa da kasa domin takaita cinikin makamai na biliyoyin kudade.

Taron majalisar ya sanya sabbin ka'idoji na safarar makaman, kama daga bindigoji samfurin Kalashnikov zuwa tankokin yaki.

Daga yanzu kasashe za su rika bayar da bayanan cinikin makaman da suka yi tare da yin cikakken nazari ko da a kan iya yin amfani da makamanta hanyar da ba ta dace ba domin cin zarafin al'umma.

Wakilan majalisar su yi ta murna da tafi yayin da aka baiyana sakamakon kuri'ar.

Kasashe uku ne kacal wadanda suka hada da Iran da Siriya da kuma Koriya ta arewa suka kada kuri'ar rashin amincewa yayin da kasashe ashirin da uku kuma suka kaurace.

Karin bayani