Majalisar dattawan Amurka ta amince da yin muhawara kan bindigogi

Baje kolin bindigogi a Amurka
Image caption Baje kolin bindigogi a Amurka

Majalisar dattawan Amurka ta kada kuri'a domin soma muhawara a kan sababbin dokokin takaita bindigogi watanni 4 bayan kisan kare dangin da aka yi wa yan makaranta da malamai a Makarantar elementare ta Sandy Hook dake Connecticut.

A cikin sauki dai aka murkushe kokarin da masu ra'ayin yan mazan jiya na jama'iyar Republican suka yi don jinkirta muhawarar .

Hakan zai kasance karon farko a cikin shekaru 20 da majalisar dokokin Amurka ta yi muhawara a kan duk wani irin takaici a kan mallkar bindigogi.

Daga cikin matakan da za'a tattauna akai har da shigo da karin hanyoyin da za'a rinka gudanar da bincike a wajen sayar da bindiga, da za a hada da hanyar sayarwa ta yanar gizo da wajen baje kolin bindigogi.

Har yanzu dai ba a kai ga yadda shugaba Obama ke son ganin an kai a matakin takaita mallakar bindiga a kasar ba, kodayake wasu 'yan kalilan daga cikin jahohin kasar sun riga sun dauka.