Wata kotu ta yi watsi da bukatar kamfanin Norvatis

INDIA
Image caption Kotun kolin India

Kotun koli a kasar India ta yi watsi da bukatar da kamfanin magani na Norvatis na kasar Switzerland ya shigar a gabanta domin neman kariya kan maganin cutar Cancer da ya inganta da ake kira Glivec.

Kotun ta ce maganin be cancanci shiga cikin magungunan da za a samarwa kariya ba, karkashin dokoki kasar saboda ba bu wani banbanci tsakaninsa da na farko da aka fitar.

Masu fafituka sun ce hukuncin kotun zai taimaka wajen ba kasashe masu tasowa damar samun magunguna masu saukin farashi.

Sai dai manyan kamfanonin magani na duniya sun ce hukuncin kotun kan iya karya lagwon yan kasuwa masu zuba jari domin gudanar da bincike