Rundunar soja a Najeriya ta kashe yan boko haram goma sha hudu

boko haram
Image caption Jami'an tsaron Najeriya

Rundunar soji a Najeriya ta ce ta kashe wasu mutane su goma sha hudu da ake zargin yan kungiyar nan da ake kira boko haram a samemen da ta kai kan wani gini a garin Kano.

Kakakin rundunar sojin kasar ya ce soja daya ya hallaka a samemen kuma sun kama wani da ake zargin dan kurnar bakin wake ne a cikin wata mota dake makare da abubuwa masu fashewa.

An dai tsaurara matakan tsaro yanzu da ake bikin Easter a wasu sasa a yankin arewacin kasar.

Daruruwan mutane sun hallaka tun bayan da mayakan kungiyar suka kara kaimi wajen aiwatar da tashe- tashen hankula.