Ana cece-kuce a kan mutuwar sojojin Afrika ta Kudu

anc southafrica
Image caption Shugaba Jacob Zuma

Mutuwar sojojin kasar Afrika ta kudu su goma sha uku a hanun mayakan yan tawaye a Bangui ya sa alamar tambaya kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka shekaru shida da suka wuce na aikewa da sojojin kasar zuwa Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

A cewar Ministan tsaron kasar Afrika ta Kudu sojoji kusan dari uku ne aka tura zuwa Jamhuriyar Afrika ta tsakiya domin su taimaka wajen samar da horo ga dakarun gwamnati.

Sai dai ya yinda yan tawaye ke danawa zuwa Bangui babban birnin kasar a ranar ashirin da hudu ga watan Maris din da ya gabata sojojin kasar Afrika ta kudu sun kasa tabuka wani abu a zo gabi saboda yan tawayen sun fi su yawa a fadan da aka shafe sa'oi da dama ana yi.

Shugabar jam'iyyar adawa, a kasar Afrika ta kudu Helen Zille , ta ce lamari ne da ke nuni da cewa kamar an aike da sojojin kasar zuwa Jamhuriyar tsakiyar Afrika ne domin su kare shugaba Francoise Bozize da aka hambararda gwamnatinsa.

Ta kuma ce an aike da sojoji ne duk da cewa kwaruru kan tsaro sun nuna rashin amincewasu bisa zargin cewa an tura sojojin domin su kare cibiyoyin kasuwancin kasar a Jamahuriyar Afrika ta tsakiya.

Madam Helen ta kuma nemi a dawo da gawawarkin sojojin daga Bangui ba tare da bata lokaci ba sanan kuma Majalisar dokoki ta gudanar da bincike kan lamari.

Karin bayani