Yara goma sha uku sun hallaka a kasar Burma

Islamin School
Image caption makarantar islamiya da gobarar ta tashi a Burma

Mutane fiye da yara saba'in ne ke barci a dakunan kwana na makarantar islamiya, a lokacin da gobara ta shi.

Rahotanin sun ce kofofin dakunan a rufe suke abin da kuma ya sa mutanen da ke ciki suka kasa fita daga dakunan, kuma hayaki ya suke su.

Ha kuma wani da ya shaida lamarin ya ce shekarun yaran sun kai 13 zuwa 14, kuma sun mutu ne saboda sun kasa durgowa daga tagogin da aka saka wa karafuna.

Sai dai 'yan sanda sun dora alhakin tashin gobarar kan wata wayar wutar lantarki da ta samu matsala.

Sun ce lamarin ba shi da nasaba da tashe- tashen hankulan baya bayanan da suka faru, tsakanin mabiya adinin Budha da kuma musulmi marasa rinjaye dake kasar.

An dai baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a wurin da lamarin ya faru, saboda jama'a da dama da suka fusata kuma ke kuka da suka taru a gurin.