Hamas ta haramta makarantar maza tare da mata

hams
Image caption Shugaban Hamas, Ismail Haniya

Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta amince da wata dokar haramta makarantar hadaka ta maza da mata a Gaza, ga daliban da suka wuce shekaru tara.

Wannan ne karon farko da za a raba dalibai a makarantun na Gaza.

Sabuwar dokar za ta soma aiki ne a wata mai zuwa.

Wani jami'in kungiyar Hamas ya ce suna kokarin tabbatar da tsarin musulunci ne a tsakanin al'ummar Palasdinawa.

Sai dai wani dan adawa ya ce matakin zai lalata tsarin ilimi.

Wannan matakin dai na zuwa ne wata gida, bayan da majalisar dinkin duniya ta dakatar da gasar gudun fanfalaki da aka shirya yi a Gaza don taimakawa kananan yara, bayan da Hamas ta ce mata ba za su shiga cikin tseren ba.

Karin bayani