An kai munanan hare hare a Afghanistan

Wasu jerin hare haren yangwagwarmaya a Afghanistan ya hallaka akalla mutane fiye da talatin a gundumar Farah dake yammacin kasar, yayin da wasu mutanen fiye da saba'in kuma sun sami raunuka yawancinsu fararen hula.

Yan gwagwarmayar sun kai harin ne akan wata kotu da gidan gwamna da kuma wasu gine ginen gwamnati dake babban birnin lardin.

An ruwaito cewa an yi musayar harbe harben bindigogi na tsawon lokaci da maharan bayan aukuwar akalla daya daga cikin harin kunar bakin waken.

Maharan sun kitsa harin ne daidai da lokacin shari'ar wasu gungungun mutane da ake zargi mayakan Taliban ne.

Lardin na Farah dake kan iyaka da Iran ya yi kaurin suna wajen tarzomar yan gwagwarmaya.