An gargadi 'yan arewa kan yawo da makami

weapons
Image caption Wasu makaman da kwace a baya bayanan a Kano

Wasu daga cikin shugabanni 'yan arewacin Najeriya mazauna yankin kudu maso yammacin kasar, sun gargadi 'yan arewa masu zuwa ci rani, su daina tafiya yankin da duk wani abu mai kama da makami.

Shugabannin sun bayyana hakan ne sakamakon yadda ake fama da matsalolin tsaro a kasar, da kuma a 'dan wannan lokacin da ake kamen mutane da dama a jihar Lagos musamman wadanda suka fito daga 'yankin arewacin kasar.

Mataimakin shugaban kungiyar tuntubar 'yan arewa a Kudu maso kudancin Najeriya Alhaji Rabiu Danjuma ya ce yadda 'yan arewa ke tahowa zuwa kudu maso kudancin kasar da makamai irinsu wuka, da takobi da kuma ada be dace ba.

Alhaji Danjuma ya ce zasu iya siyan kayyayakin idan sun iso yankin kuma su yi rajista da mahukuntan yankin saboda hakan zai kawarda duk wani zargi da za a yi mu su