Matasa a Pakistan sun fi son shariar musulunci a kasarsu

Pakistan
Image caption Wasu matasa a Pakistan

Wani sabon bincike da aka gudanar kan matasa a kasar Pakistan ya nuna cewa da dama daga cikinsu sun yi ammana cewa tsarin mulkin dimokradiyya be dace da kasarsu ba.

A ganinsu tsarin mulki shari'a ce ta dace da kasar, yayinda mulkin soja shi ne na biyu.

Bincike da cibiyar raya al'adun Birtaniya wato British Council ta gudanar ya nuna cewa kashi casa'in cikin dari na matasan kasar na ganin kasar na tunkarar wata turba ne marasa kyau.

Sama da mutane dubu biyar masu shekaru tsakanin goma sha takwas zuwa ashirin da tara ne dai aka tambaya a sassa da dama na kasar gabanin zaben gama gari da za a yi a cikin makonni masu zuwa