Kotu ta ci tarar Air France saboda nuna wariya

air france
Image caption Jirgin Air France ya ce zai daukaka kara

Wata kotu a Faransa ta sami kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Air France da laifin nuna wariya, tare da cin shi tarar dala dubu 16 bisa cire wata maata mai fafitikar kare Hakkin Falasdinawa daga cikin wani jirginsa da zai kaita Isra'ila saboda ita ba Bayahudiya ba ce ko kuma 'yar Isra'ila.

Horia Ankour, wadda daliba ce, tana shirin zuwa birnin Tel Aviv daga Faransa a bara, domin haduwa da wasu masu fafituka, don gudanar da wani kanfe na goyon bayan Falasdinawa.

Amma sai aka cire ta daga cikin jirgin saman da zai kai ta can, bayan da wani ma'aikacin jirgin ya tambaye ta ko ita BaYahudiya ce ko kuma 'yar Isra'ila ce, amma sai ta ce a'a.

Kamfanin na Air France dai ya ce tana cikin jerin sunayen mutanen da Isra'ila ta ce ba ta bukatar su shigo cikin kasar ta, kuma kamfanin ya ce zai daukaka kara.