Amurka na kamfen tsaurara mallakar bindiga

Image caption Obama na kamfe din tsaurara mallakar bindiga

Ana sa ran karamar majalisar dokokin Amurka ma za ta amince da shirin dokar tsaurara mallakar bindiga a kasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake jimamin harbe kananan yara ashirin da malaman su shidda a jihar a cikin watan Disambar bara.

A halin da ake ciki kuma a Kamfe da Shugaba Obama ke yi na neman a kafa dokoki masu tsauri na rike bindiga ya isa jihar Colorado, a dab da gidan Silima din da wani dan bindiga ya harbe mutane goma sha-biyu a bara.

Lokacin da ya ke magana a Kolejin horon 'yan sanda ta Denver, ya ce dokokin da jihar Colorado din ta kafa tun lokacin da aka yi wannan harbi sun nuna cewar tsaurara bincike a kan mutane ba zai keta hakkokin mutanen dake rike bindigogi ba, wadanda su ka san abin da suke yi.

A yanzu haka kashi casa'in na mutanen Amurka sun goyi bayan mataki mai tsauri, abin da zai hana miyagun mutane mallakar bindigogi.

Karin bayani