Shugaba Jonathan ya gana da jami'an tsaron Najeriya

Image caption Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar yi wa yan Bokoharam afuwa

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeria yayi wata ganawa tare da shugabannin hukumomin tsaro na kasar.

Ganawar ta su dai ta biyo bayan gawanar da shugaban ya yi ne a jiya da dattawan arewacin kasar.

A ganawarsa da dattawan arewacin kasar dai sun tattauna a kan matsaloli da ke addabar arewacin kasar da kuma batun yiwa 'yan kungiyar nan ta Jama'atu Ahlus Sunna Lid Da'awati wal Jihad wadda aka fi sani da Boko haram Afuwa.

Barrister Solomon Dalung, yana daya daga cikin dattawan arewa da suka gana da Shugaban kasar, kuma ya shaidawa BBC cewa Shugaba Good Luck zai yi taron gaggawa na tsaron don duba batun.

Tun farko dai Sarkinmusulmi Sa'ad Abubakar ya yi kira g shugaban kasar ya yi wa 'yan Kungiyar Boko Haram afuwa.

Sai dai gwamnatin bata dauki wannan kira da mahimmanci ba, sai dai ko wannan karon za ta sake zani; abu ne da lokaci zai nuna.

Karin bayani