Sama da mutane dubu uku ne aka kashe a Ivory Coast

Hukumomi a kasar Ivory Coast sun soma aikin tono gawarwakin mutanen da suka rasu sakamakon tashin hankalin daya biyo bayan zaben shugaban kasar a shekara ta 2010.

Fiye da mutane dubu uku ne suka mutu sakamakon rikici tsakanin magoya bayan zababben shugaban kasar, Alassane Ouattar da kuma magoya bayan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo wanda yaki yarda ya sauka daga kujerar mulki.

Jami'an tsaro dana majalisar dinkin duniya sune suka tsaye a kusada kaburburan , a yayinda malaman addinai suka yi addu'oi kafin a soma tono gawarwakin.

A wani kabari dake kusada wani masallaci a Yopougon lardin da akwai 'yan gani kashenin Laurent Gagbo an tono gawarwakin wasu mutane maza su hudu wadanda shekarunsa yake daga 17 zuwa 35, kuma an kashesu ne saboda sun yi kokarin kare masallaci daga wajen magoya bayan Lauren Gbagbo.

Iyalan mamatan sun tsaya jugum lokacin da ake tono gawarwakin.

Ministan Shari'ar kasar Ivory Coast ya ce akwai kaburbura 57 irin wannan da aka binne mutane da dama, kuma dole ne sai sun tona duka.