Amurka na fuskantar barazana daga Koriya ta arewa

Rasha ta yi Allah Waddai da Korea ta Arewa bisa barazanar da ta yi na kaddamar da hare-haren nukiliya a kan Amurka.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha, ya zargi Korea ta Arewan da laifin rena kudurorin MDD, tare da yin gargadin cewa matakin zai iya kawo cikas ga yiwuwar koma wa teburin shawarwari kan shirinta na nukiliya.

Tun farko dai Korea ta Kudu, ta ce Korea ta Arewa ta girke wani makami mai linzami mai dogon zango a gabar ruwanta dake gabashin tsibirin.

Wannan al'ammari na baya-baya dai ya zo ne yayinda Amurka ta karfafa matakan tsaronta na kariya daga makamai mazu linzami a kewayen sansaninta dake tsibirin Guam na tekun Pacific, tana mai cewa barazanar da ake fuskanta daga Korea ta Arewa, wani babban hadari ne.