An gano zamba a na'urorin ATM

ATM

An samu karuwar zamba ta hanyar na'urorin dake amfani da tikiti a fadin kasashe biyar dake nahiyar Turai.

Mazambata na amfani da wani kati wanda suke likawa a mashinan cirar kudi na ATM da makamantansu, inda mutane ke amfani da katin kudinsu.

Masu wannan danyen aikin, sun fi amfani da na'urorin tikiti na jiragen kasa da na Bas-bas da gidajen mai da kuma inda ake biyan kudaden ajiye motoci.

Bayanan da suka tattara ana amfani da su a wasu kasashen kamar Amurka, inda ba a da tsarin kariya mai karfi.

ReDigi

Wani kamfani dake barin mutane su saya tare da sayar da wakokin da ba a riga an mallaka ba, ya sha kaye a wata kara game da 'yancin mallaka a Amurka.

ReDigi na son ya sake kirkirar wata hanyar kasuwanci na sayar da wakokin da aka yi a baya a shafukan intanet, kuma a hukumance ya goge ainihin wakar kafin ya tura wa wanda ya sayarwa.

Sai dai kotun ba ta amince da hakan ba, inda ta yanke hukuncin cewa tun da za a wanki wakar, ba zai yiwu a musanya faifai a shafin intanet kamar yadda ake musayar littafi ko faifan dvd a zahiri ba.

Baidu da Google

Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, domin abin da tun farko ake kallo kamar wani barkwanci ne da ake yayatawa a shafukan internet cewa katafaren kamfanin intanet na China, Baidu na aiki a kan fasahar tabarau mai kama da na Google ya tabbata.

Wani kakakin Baidu ya ce kamfanin tuni ya na da karamin gilashin da ya kammala.

Twitter

Dandalin sada zumunta na Twitter ya sanar da shirin cajin dala biyar a duk wata ga masu amfani da wasula a shafin.

Domin kada a bar shi a baya, kamfanmin matambayi baya bata na Google ya kaddamar da wata fasaha ta Google Nose, wanda ta hanyarsa masu ziyarar shafin za su iya jin kanshi.

Bugu da kari - manhajar na baiwa mutane zabi wurin bincike wato SafeSearch.