Kasashe 6 za su sake tattaunawa da Iran

Image caption Za a sake tattaunawa da Iran kan shirin ta na nukiliya

Jami'ai masu kokarin sasanta batun nukiliya daga manyan kasashen duniya shida na shirin fara wani zagayen tattaunawa da Iran dangane da shirin nan na ta da ake cece-kuce na nukiliya.

Kasashen shida da suka hada da Amurka da Rasha da China da Faransa da Birtaniya da Jamus za su gana ne da wakilan kasar ta Iran a birnin Almaty na Kazakh.

Ana sa ran za su gaya wa Iran din ne ta amince da tayin farko da aka yi mata na sassauta mata wani bangare na takunkumin da aka sanya mata na tattalin arziki, idan dai har ta dakatar da aiki a wasu sassa da ake ganin masu hadari ne, a shirin ta na nukiliya.

Masu nazarin lamura sun ce yayin da Iran din ke shirin zaben Shugaban kasa a watan Yuni, shawara irin wannan mai sarkakiya da wuya ta samu karbuwa.

Karin bayani