Rikicin Korea zai iya zama bala'i – Moon

Image caption Moon ya yi gargadin hadarin dake tattare da yakin Korea

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki- Moon, ya yi kira ga Korea ta Arewa ta sassauta barazanar da ta ke yi ta amfani na makaman nukiliya.

Ban ki-Moon, ya na mai cewa Korea ta arewar ta wuce gona da iri.

Lokacin da ya ke magana a wani taron manema labarai a birnin Madrid, Mr Ban, ya yi kira ga Korea ta Arewa ta sassauta barazanar ta.

Mr Ban din ya ce, zaman lafiya da tsaro a yankin na Korea yana da matukar tasiri ga yankin da ma duniya baki daya.

Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya ce damuwarsa ita ce, duk wani kuskure da aka yi cikin lamarin zai iya haifar da mummunan sakamako.

Ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin dake da hannu a hayaniyar ta yankin Korea, su sasanta su mayar da wukaken su kube.

Tun farko dai Korea ta Arewa ta ce ta baiwa sojojin ta umarni na karshe su kaddamar da hari kan Amurka, idan ma ta kama da makaman nukiliya.

Tuni dai Korea ta arewar ta kai wasu makaman masu dogon zango gabar ruwa ta gabashin kasar ta.

Karin bayani