Koriya ta Arewa ta ce a kwashe jami'an diplomasiyya

Image caption Shugaba Kim Jung-un

Koriya ta Arewa ta bayyanawa ofisoshin jakadancin kasashen waje ciki hadda na Rasha da kuma Birtaniya dake Pyongyang su duba yiwuwar kwashe ma'aikatansu daga cikin birnin.

Ofishin hudda da kasashen waje na Birtaniya a London ya na nazarin matakan da zai dauka nan gaba.

Wannan matakin ya biyo bayan rahotanni daga Koriya ta Kudu dake cewar Koriya ta Arewa ta riga ta girke wasu makamai masu lunzami tana jiran kota kwana.

Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya amtabo wani babban jami'in soji na cewar an dauki makaman masu linzami ta jirgin kasa zuwa wajen da za a dunga harba su dake gabar tekun gabashin Koriya ta Arewa.

Karin bayani