Paparoma Francis na son kawarda cin zarafin yara.

pope
Image caption Paparoma Francis

Paparoma Francis ya yi kira ga Cocin Roman Katolika ya dauki mataki kwakwara na magance matsalar cin zarafin kananan yara.

Wannan dai shi ne kalaminsa na farko a kan wannan batu tun bayan da ya zaman Paparoma.

Paparoman ya yi kira a hukunta duk wadanda suka aikata irin wannan laifi, yana mai cewa hakan yana da mihimmanci domin kare martabar Cocin.

Paparoma Francis dai ya hau kan mukaminsa ne a daidai lokacin da Cocin ke farfadowa daga wasu jerin abubuwan kunya da suka shafi lalata da kananan yara da ake zargin wasu mabiya darikar da aikatawa.

Karin bayani