Amurka ta waske wa barazanar Korea

Image caption Korea ta arewa a shirye take ta gwabza yaki

Amurka ta yi wani kokari na sassauta barazanar yaki a tsibirin Korea bayan Korea ta Arewa ta shafe makonni tana wasu kalamai na barazanar kai farmaki a kan Amurkar.

Kakakin Fadar gwamnatin White House Jay Carney, wanda ke amsa tambayoyin manema labarai a game da batun makamai masu linzami da aka ce Korea ta Arewa ta giggirke, ya ce ba zai yi mamaki ba idan Korea ta Arewa ta yi gwajin makamin mai linzami.

Ya ce,"Muna sa ido sosai kan al'amurran dake gudana kuma ba za mu yi mamaki ba idan sun dauki irin wannan matakin.

Rundunar sojan Amurka ta ce kalaman na Korea ta Arewa abin damuwa ne - amma dai ga alama ba su nuna alamar yaki gadangadan ba - sai dai tsokana.

Karin bayani