Sudan ta kudu ta soma fitar da mai

Kasar Sudan ta Kudu ta sake soma fitar da man ta, abin da ya kawo ƙarshen rikicin da ta kwashe watanni goma sha biyar ta na yi da Sudan, abin da ya jawowa kasashen biyu asarar kuɗaɗen shiga na biliyoyin daloli.

A farkon shekarar da da wuce ne Sudan ta Kudu ta dakatar da hakar mai bayan da ta zargi makwabciyarta Sudan da tsawwala kudadan fito na tura man zuwa kasuwannin dudiya ta tashar ruwan Sudan din.

Yayin da aka dawo da hakar mai a Sudan ta kudu, ministan mai na kasar, yace, ya kamata a dauka cewa, dawo da harkokin hakar mai wata alama ce ta wanzuwar zaman lafiya.

A baya dai dangantaka tayi matukar tabrbarewa tsakanin Sudan ta kudun da makwabciyarta jamhuriyar Sudan dangane de batun mai, har sai da ta kai ana tunanin yaki zai barke tsakanin sassan biyu.

Yayin da Sudan ta kudu ta samu 'yan cin kai kusan shekaru biyu da suka gabata, ta kwashe kusan kaso mai tsoka arzikin man dake Sudan. Sai dai kuma saboda yanayin kasar ta Sudan ta kudu dole ta dogara da tashoshin jiragen ruwa na jamhuriyar Sudan wajen fitar da manta zuwa kasuwannin duniya.