Hare haran NETO ya hallaka yara a Kunar

Hari a A fghanistan
Image caption Hari a A fghanistan

Mutane da jami'ai a lardin Kunar na Afghanistan sun ce an kashe yara 10 a wani hari da dakarun NETO suka kai ta sama a kauyuka 3 na lardin.

Mazauna kauyukan sun ce yaran sun mutu ne lokacin da rufun kwanon gidansu ya rufta bayan da aka jefa bam a wajen dake kusa da iyaka da Pakistan.

Har ila yau mata biyu da masu tada kayar baya da dama ne aka kashe a harin.

Dakarun hadin guiwa na kasa da kasa wato ISAF sun ce ba su da wani rahotan mutuwar fararan hula a harin amma suna gudanar da bincike.

Batun kashe fararan hula a hare haran da NETO ke kaiwa ya kasance wata babbar matsala tsakanin jami'an Amurka da na Afghanistan.

Karin bayani