An dauki bakaken fata tamkar karnuka a Mumbai

Sambo da Sheeba
Image caption Sambo da Sheeba

'Yan Afrika da dama da ke zaune a babban birnin kasuwancin kasar India Mumbai (Bombay), suna koka wa game da wariya da kuma matsin lamba da 'yan sanda ke yi musu.

Wani dan Najeria Sambo Davis da ke auren wata mata 'yar India na daga cikin 'yan Afrikan da ke zaune a Mumbai.

Yana da cikakkun takardun izinin zama a India, sai dai 'yan sanda sun kama shi kwanakin baya bisa zargin yana safarar miyagun kwayoyi.

An dai tsare shi tare da wasu 'yan Afrika bakaken fata 30 har tsawon sa'o'i da dama, kafin daga bisani aka sake tare da basu hakuri.

Sai dai Davies ya ce, ya yi mamaki kashe gari da ya karanta a jaridu cewa an kama su ne bisa laifin ta'ammali da miyagun kwayoyi.

" 'Yan sanda na ganin mu tamkar karnuka ne a garin nan," in ji Davies.

Mr Davies ya kuma ce ana nuna masa wariya idan ya je gidajen cin abinci, ko kuma ya yi yunkurin kama gidan haya a yankin masu hannu da shuni a birnin.

Sai dai ya yi sa'a, saboda ya samu gida mai kyau, sakamakon yana auren 'yar kasar ta India.

Sai dai 'yan uwansa 'yan Najeriya, na ci gaba da fuskantar matsala idan sun je neman gidan haya, ana ce musu " ku bakaken fata ne, ku 'yan Najeriya ne, ko kuma ba ma bukatar ku a nan. Wannan nuna wariyar launin fata ne."

'Wasan buya'

Babu dai wata kididdiga da ke nuna ko 'yan Afrika nawa ne ke zaune a Mumbai, sai dai tun lokacin da tattalin arzikin India ya fara bunkasa, da dama sun zo suna aiki a ciki da kewayen birnin. Wata kididdiga da ba ta hukuma ba, ta nuna cewa yawansu ya fi dubu biyar.

Da dama na kasuwancin fitar da tufafi zuwa Najeriya da sauran kasashen Afrika ne.

Wasu kuma dalibai ne da ke karatu a muhimman makarantun yankin.

Sai dai kuma akwai daruruwan 'yan Najeriya da ke zaune a matsayin bakin haure a India. Wasunsu ko dai sun batar da fasfo dinsu, ko kuma biza ta izinin zamansu a kasar ta kare.

A kullum irin wannan mutanen na yin wasan buya ne da 'yan sanda - domin da zarar an kama su, ana tura su kurkuku ne.

Ikeorah Junior daga jihar Legas a Najeriya, yana kula da wani shagon shan gahawa na 'yan Afrika a wata kasuwa mai yawan jama'a a titin Mohammed Ali da ke Mumbai.

Ya ce " Ban san daililin da ya sa 'yan sanda ke bi gida-gida domin kama mutanen da ba su da cikakkun takardun izinin zama a kasar nan ba. Idan ba su da takardun izini zama, sai ku tasa keyar su zuwa kasashensu, maimakon ajiye su a kurkuku."

Ahmed Javed, wanda shi ke kula da aikin samar da tsaro da zaman lafiya a jihar Maharashtra ya ce batun ba mai sauki ba ne.

"A lokuta da dama ba su da Paspo, sai idan an tabbatar da kasarsu ta ainihi ne za a iya tasa keyar su zuwa gida." In ji Ahmed.

'Yan Afrika da dama suna zaune ne a yankin Mira Road, wani yanki mai kura da ke a wajen garin Mumbai.

Daya daga cikinsu wanda bakon haure ne, ya roke ni kudi, yana mai cewa kwanansa biyu bai ci abinci ba.

Yana cike da damuwa, domin ya ce masu safarar miyagun kwayoyi sun tuntube shi da ya zo ya yi musu aiki.

"Shekara ta uku a nan - biza ta ta kare tun da jima wa. Ina son koma wa gida. Don Allah ka taimake ni dan uwa," in ji shi.

A yankin da yake, kalmar Negro ko kaalia (wadda ke nufin bakin mutum a yaren Hindu) sune kal momi biyu da ake amfani da su wajen kiran dukkan bakaken fata.

"Muna kiransu Negro ne domin bakaken fata ne. Kamanninsu na bamu tsoro," in ji wata mata 'yar asalin India.

Abin kunya

Sai dai duk da wannan wariyar da ake nuna wa, Sheeba Rani ta auri Sambo Davis shekaru hudu da suka gabata, kuma a yanzu suna da 'ya'ya biyu.

Sheeba ta ce iyayenta sun amince da aurensu, sai dai abokai da 'yan uwa na ta tsangwamar ta tun da suka yi aure.

Ta ce abin kunya ne yadda 'yan uwanta 'yan India ke mu'amulla da bakaken fata.

Sai dai duk da wulakancin da ake yi wa bakaken fata, kusan dukkan 'yan Afrika da BBC ta zanta da su sun ce sun son zama a kasar ta India.

Suka ce dangantaka tsakanin India da Afrika na da kwari.

Da damansu sun ce 'yan India da 'yan Afrika 'yan uwan juna ne.