Mandela ya yi kwana daya a gidansa

Image caption Mandela ya kwana daya a gidansa bayan ya fito daga asibiti

Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela ya kwana gidansa dake Johannesburg a yau, Lahadi a ranar farko bayan sallamar sa daga asibiti wurin da ya shafe kwanaki goma ana yi masa maganin cutar Lamonia.

Gwamnatin Afrika ta Kudu ta ce tsohon Shugaban kasar mai shekaru casa'in da hudu yana murmurewa za a kuma cigaba da kula da shi a gidansa.

Mr Mandela ya yi fama da rashin lafiya iri-iri a 'yan watannin nan.

Matsalar da yake fama da ita ta cutar huhu ta fara riskar sa ne lokacin da ya shafe shekaru ashirin da bakwai a gidan Yari a zamanin yaki da wariyar launin fata.

Karin bayani