Ana taron gina Dafur na Sudan a Qatar

Image caption Ana kokarin gina yankin Dafur da yaki ya dai dai ta

Masu ba da agaji na kasa da kasa suna hallara a kasar Qatar a ranar farko ta taron kwana biyu da za su yi na tattauna batun rayawa da sake gina yankin Dafur na Sudan da yaki ya daidaita.

Taron wani bangare ne na yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma a baya-bayan nan ta kokarin farfado da zaman lafiya a yankin na Darfur shekaru goma bayan barkewar rikici a lokacin da 'yan tawaye wadanda mafi rinjayensu ba Larabawa ba ne suka yi wa gwamnatin Sudan bore.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa an kashe a kalla mutane dubu dari uku a dalilin rikicin yayin da wasu mutanen kimanin miliyan biyu suka tsere daga gidajensu.

Karin bayani