An tara makudan kudade domin raya Darfur

Wata mata a yankin Darfur
Image caption Wata mata a yankin Darfur

Taron gidauniyar da aka yi a Qatar domin tallafawa yankin Dafur dake fama da rikici ya tara tsabar kudi dala biliyan uku da miliyan dari shida na alkawuran kudade domin raya cigaban yankin.

Za'a yi amfani da kudin ne a shirin raya kasa na shekaru shida da za'a aiwatar a yankin.

Alkaluman sun hada da alkawuran da gwamnatin Khartoum ta yi a karkashin 'yarjejeniyar zaman lafiya da ta sanyawa hannu a shekarar 2011.

Kudaden za su taimakawa Dafur samun wadatar abinci da tallafin jin kai domin raya yankin.

Karin bayani