An kashe sojoji da 'yan gwagwarmaya da dama a Pakistan

Tashin hankali a Pakistan
Image caption Tashin hankali a Pakistan

Jami'an soji a Pakistan sun ce akalla sojoji talatin ne da 'yan gwagwarmaya kimanin dari daya aka kashe a mummunan dauki ba dadi a yankin Koramar Tirah dake arewa maso yammacin Pakistan.

Jami'an suka ce sojoji sun karbe ikon mafi yawancin yankuna a lardin daga hannun 'yan Taliban da aminansu tun bayan da suka kaddamar da farmakin kasa a ranar Juma'ar da ta wuce.

A yan makonnin nan kungiyoyi dake gaba da juna suna ta gwabza fada a tsakaninsu domin karbe ikon yankin.

Ya zuwa yanzu mutane kusan dubu arba'in ne suka yi kaura daga yankin domin tsira da rayukansu.