Tarihin Rayuwar Margaret Thatcher

Margaret Thatcher
Image caption Tsohuwar Priyi Ministar Birttania

An haifi Margaret Hilda Thatcher ne ranar 13 ga watan Oktobar shekarar 1925 a Grantham, Lincolnshire.

Mahaifinta shine Alfred Roberts. Mutum ne mai wa'azin addinin Kirista kuma kansila ne na karamar hukuma. Yayi matukar tasiri a rayuwarta da kuma irin manufofin data rika aiwatarwa a lokacin da take rike da mukamin Pryi Ministar Burtaniya.

Marigayiya Margaret Thatcher dai ta karanta fannin kimiyyar hada sinadarai ne a kwalejin Somerville dake Oxford, inda ta kasance mace ta uku data taba rike mukamin shugabar kungiyar dalibai masu ra'ayin rikau a jami'ar Oxford.

Bayan kammala karatunta ne Magret Thatcher ta fara aiki a wani kamfanin sarrafa robobi kana kuma ta shiga harkokin siyasa, inda a shekarar 1949, aka tsayar da ita takarar kujerar 'yar Majalisa a Jam'iyar Conservative daga mazabar Dartford a Kent inda ta sha kaye a manyan zabubbukan da aka gudanar a shekarun 1950 da kuma 1951.

To sai dai kuma tauraruwarta a fannin siyasa ta fara haskakawa saboda yadda ta zama 'yar takarar mafi kankantar shekaru data fito daga jam'iyar Conservative, yayin da a shekarar 1951 ta auri Denis Thatcher, inda kuma ta ci gaba da karatun fannin shari'a data kammala a shekarar 1953, shekarar data haifi 'ya'yanta na farko 'yan biyu wato Mark da Carol.

Sannu a hankali dai an ci gaba da damawa da Magret Thatcher a harkokin siyasar cikin gida a Burtaniyar inda har aka kai ga nadata mukamai dabam dabam da suka hada da sakatariyar ilimi data kula da muhalli.

A shekarar 1979 ne dai likkafa ta yi gaba inda marigayiya Margaret Hilda Thatcher tayi nasarar darewa mukamin Pry Minista a Burtaniya bayan nasarar da jam'iyarta ta samu a babban zaben kasar.

A lokacin da take rike da mukamin Priyi Minista dai marigayiya Magret Thatcher ta yi ta kokarin ganin ta aiwatar da wasu muhimman sauye sauye a bangaren tattalin arzikin kasar.

Kasancewarta mace ta farko da taba darewa mukamin Priyi Minista a Burtaniya, Marigayi Magaret Thatcher dai ta yi kokarin kawo sauye sauye a harkokin siyasar kasar inda ta bullo da wasu sauye na ba-sani-ba-sabo a fannoni dabam dabam, matakin da yasa ta yi kaurin suna har ta kaiga ana kallonta a matsayin shugabar da aka fi kauna kana kuma aka fi tsana a Burtaniya.

Karin bayani