" Zaman lafiya a arewacin Najeriya na hannun gwamnoni"

gwamna
Image caption Shugaban gwamnonin arewacin Najeriya, Dr Muazu Babangida Aliyu

Malam Adamu Ciroma ya ce tun da shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan, ya kafa kwamitin duba yiwuwar yiwa 'yan kungiyar Ahlissuna Lidda'awati wal Jihad da ake kira Boko Haram, afuwa, saura gwamnoni su taka tasu rawar.

Malam Adamu wanda, daya ne daga cikin dattawan yakin Yace a yanzu ya rage ga gwamnonin yankin su taka rawar da ta dace don kawo karshen zubar da jini.

Malam Adamu Ciroma wanda tsohon ministan Kudi ne ya bayyana haka ne a cikin wata hira da sashin Hausa na BBC.

A cewarsa batun samun zaman lafiya abu ne da ya fi shafar Jihohi, don haka ya kamata Gwamnonin su maida hankali kan tabbatar da shi a jihohinsu.

Karin bayani