Boko Haram ta yi watsi da shirin afuwa

Wasu da ake zaton 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne Hakkin mallakar hoto s
Image caption Kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal jihad ta ce ita ya kamata ta yiwa gwamnatin Najeriya ahuwa

Kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram, ta yi watsi da shirin yi musu afuwa da gwamnatin Najeriya ke yi, suna cewa su aka yi wa laifi amma ba su suka yi laifi ba.

Wata sanarwa da ta fito daga shugaban kungiyar Abubakar Shekau ta ce idan ma afuwar ne sai dai su su yi wa hukumomin Najeriya afuwar.

Tuni dai gwamnatin ta kafa wani kwamiti da zai duba yiwuwar yi wa 'yan kungiyar ta Boko Haram afuwa sakamakon kiraye-kirayen da bangarori da dama ke yi na a yi musu afuwa domin su fito su ajiye makamansu.

Kungiyar ta ce tana yakar gwamnati ne domin su dauki fansar kashe-kashen musulmai da kame musu mata da cin zarafinsu da aka yi a garuruwan Pilato, da Zongon Kataf da sauransu.

Tuni dama batun yi wa 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram afuwa na ci gaba da janyo kace-nace a Najeriyar.

Yayinda gwamnatin Najeriya ke duba yiwuwar yi wa 'ya'yan kungiyar afuwa sakamakon matsin lamba daga bangarorin wasu 'yan kasar musamman dattijan arewa, wasu 'yan kasar musamman kungiyar Kiristoci sun yi fatali da shirin, inda suka ce 'ya'yan kungiyar ba su cancanci a yi musu afuwa ba saboda kashe-kashen da suke yi.

A yanzu dai za jira ne a ga irin martanin da bangarorin za su mayar game da wannan matsayin da 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram suka dauka na watsi da shirin afuwar da kuma irin tasirin da hakan zai yi ga shirin yin afuwar na gwamnatin tarayya.