An cinye rakumin shugaban Faransa a Mali

Shugaba Hollande a lokacin da aka bashi kyautar rakumin
Image caption Faransa ta fara janye dakarunta daga Mali

Jami'ai a kasar Mali sun ce za su kara aika wa shugaban Faransa, Francois Hollande kyautar wani rakumi, bayan wadanda aka ba ajiyar na farko sun dafa sun cinye.

Mali ta bayar da rakumin farko ne domin nuna godiya ga Faransa, saboda tura sojojinta da tayi aka fatattaki masu fafutukar Islama a arewacin kasar.

Kuma an baiwa Mr. Hollande rakumin ne a lokacin da ya kai ziyara Timbuktu, a watan Fabrairun da ya gabata.

Sai dai maimakon a kai rakumin Faransa a ajiye shi a gurin ajiye namun daji, sai masu taimakawa shugaban kasar suka yanke shawarar ba wani iyali rakumin domin su kula da shi.

Amma sai iyalin suka yanka rakumin suka cinye.

A yanzu dai hukumomi a Mali sun ce, za su kara aika wani rakumin wanda yafi wancan girma da kuma kyau birnin Paris.