Cameron ya jinjinawa Margayi Thatcher

camron
Image caption Pirayi Minista, David Cameron

Firaministan Birtaniya David Cameron ya jinjinawa Margaret Thatcher wadda ta rasu a ranar litinin da ta wuce da cewa shugaba ce gwarzuwa wadda ta kara habaka karfin tasirin Birtaniya.

Firaministan ya yi yabo ne yayin wani zama na musamman na majalisar dokoki domin karrama marigayiyar.

Mista Cameron ya tunato da cewa yawancin abubuwan da ta dage ta yi gwagwarmaya akai ana cin moriyarsu har yanzu.

A nasa bangaren jagoran adawa Ed Miliband ya yabawa Thatcher bisa fahimtar muradun al'ummar Birtaniya.

Sai dai kuma wata 'yar siyasar ta jam'iyyar Labour Glenda Jackson, nuna takaici ta yi da rashin nuna tausayi ga masu karamin karfi da gwamnati karkashin Margaret Thatcher ta yiwa jama'a.

Karin bayani