Yara aka fi yiwa fyade- Save the Children

Image caption Yara na fuskantar matsalar fyade a lokacin yaki da bayan yaki inji Save the Children.

Kungiyar tallafawa yara ta Save the Children ta ce yawancin wadanda ake cin zarafi da fyade a lokacin yaki yara ne.

An dai tabbatar da hakan ne bayan nazarin da akayi akan wasu kasashe da ake yaki shekaru goma da suka gabata wanda suka hadar da Colombia da Liberia da Jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

Gwamnatin Burtaniya ta ce za ta maida hankali a kan matsalar fyade a inda ake yaki, a lokacin da ta hau kujerar shugabancin kungiyar G8 a farkon wannan shekarar.

Kungiyar ta save the children ta kuma ce wannan batu na yiwa yara fyade a kasashen da ake yaki na cikin abubuwan da za'a tattauna a taron Ministocin harkokin kasashen waje na kungiyar G8 da za a fara a yau dinan.

Wani bincike da aka yi a kasar Liberia wadda a yanzu haka take farfadowa bayan yankin basasar da aka yi kasar ya yi nuni da cewa sama da kashi takwas din mutanen da aka yiwa fyade a kasar 'yan kasa da shekaru goma sha bakwai ne.

Kungiyar Save the Children ta ce alkaluma sun banbanta tsakanin kasashen musamman ind aka yi yaki shekaru goma da suka wuce.

Kungiyar ta ce yara ne akewa fyade a lokacin yaki da kuma bayan yaki sannan kuma ana garkuwa da yara mata da maza.

Bincike dai ya nuni da cewa tunanin fyaden yana damunsu a rayuwarsu idan sun girma.

Kungiyar Save the Children ta ce shire-shiren da aka bullo da shi domin taimakawa irin wadannan yara na fuskantar koma baya saboda babu isassun kudaden gudanarwa.

Jami'an gwamnatin Burtaniya na fatan taron Ministocin na G8 zai maida hankali wajen duba laifukan da su ka danganci fyade da kuma ganin a tsananta bincike.