Bakin haure sun yi gangami a Amurka

Image caption Bakin haure na neman a basu takardun shaidan 'yan kasa a Amurka

Ma'aikata da basu da takardun izinin zama a Amurka sun gudanar da wata zanga-zangar lumana, domin neman majalisar dokokin kasar ta amince da wasu sauye-sauye na shige da fice.

'Yan Majalisar dai na tattaunawa a kan batun da ya kai kusan shekarun hamsin ana cece kuce a kansa.

Sauye-sauyen dai zai samar da takardar shaidan dan kasa ga kusan bakin haure miliyan goma sha daya a Amurka wadanda su ka shiga kasar ba bisa ka'ida ba da kuma tsaurara matakan tsaro a kan iyakoki.

Dubun dubatar bakin haure ne da kuma kungiyoyin farar hula su ka taru a Washington da kuma sauran birane a Amurka domin nuna bukatar su ga Majalisar dokokin Amurka na amincewa da sabuwar dokar shige da fice a kasar.

A baya dai akwai yunkurin da aka yi ta yi na ganin a yin garan bawul ga dokokin shige da fice a kasar inda har a shekara ta 2007 shugaba George Bush da wasu 'yan majalisa su ka yi kokari yin sauyi amma daga baya ya faskara.

Shugaba Obama dai ya sha alwashin aiwatar da sauyin a harkar shige da fice a mulkinsa a karo na biyu.

Yunkuri tsaurara matakan tsaro a kan iyakar Mexico dai zai taimakawa wajen samar da goyon baya daga 'yan Majalisar Jam'iyyar Republican.

Akwai wadanda ke adawa da dokar, inda suka ce baiwa bakin haure takardu shaidar kasa zai zai kawo cikas ga 'yan kasa wajen samu aikin.

Wadanda kuma ke goyon bayan sauyi cewa suke yi yawancin aikin da bakin haure ke yi 'yan asalin Amurka din ba za su iya yi ba.