Gwamnatin Syria na kai hari ga fararen hula

Image caption Human Rights Watch ta zargi sojin sama a Syria da kaiwa fararen hula hari da gangan

Kungiyar kare hakin dan adam ta Human Rights Watch ta zargi gwamnati Syria da kaiwa fararen hula hari da gangan.

Kungiyar ta ce tana da shaidar kusan wurare hamsin da gwamnati ta kashe fararen hula wanda hakan ke nufin cewa ta aikata laifukan yaki ne.

Sojin saman Syria sun fara yaki ne da 'yan tawaye a watan Yulin bara kuma tun daga wannan lokacin ta ci gaba da kai hari a kusan kullum ga sassa daban-daban na kasar in ji Kungiyar Human Rights Watch.

Kungiyar ta ce mutuwar fararen hula a kasar ba wani abun boye bane a yayinda ta ce binciken da ta gudanar shine mafi girma a kwanan.

Human Rights Watch ta ce an kashe sama da fararen hula dubu hudu a Syria a bana.

Masu binciken kungiyar sun ce sun ziyarci kusan wurare hamsin da ke karkashin ikon 'yan tawayen a arewacin Syria, inda suka tabbatar da mutuwar fararen hula dari da hamsin a yayinda suka ce babu dan tawaye ko daya a cikinsu.

Kungiyar ta zargin sojin sama da kai hari kan wasu da ke layin siyan biredi da kuma asibitoci biyu da gangan.

Har wa yau akwai fararen hulan da aka kashe da dama da manyan makamai da kuma bama bamai harma da harin da ake kaddamarwa da jirage masu saukar angulu.

Kungiyar ta ce wadannan hare-hare da ake kaiwa fararen hula laifukan yaki ne.

Binciken na Human Rights Watch ya duba larduna uku ne a kasar, amma binciken shine mafi girma a kasar duk da cewa wani dan karamin bangare ne a kasar.

Har wa yau, kungiyar ta soki 'yan tawayen saboda kafa sansani da suke yi kusa da inda fararen hula ke zama, amma ta ce hakan ba dalili bane na kai wa fararen hula hari.