G-8 ta yi alkawarin shawo kan matsalar fyade a lokacin yaki

William Hague
Image caption Mr Hague ya ce kungiyar G8 za ta bayar da dala miliyan 35 don yaki da matsalar

Kungiyar kasashe takwas da suka cigaba ta fuskar masana'antu, wato G8 ta yi alkwarin daukar matakan kawo karshen amfani da fyade a matsayin wani makami a lokacin yaki.

A taron kungoyar da ake yi a London, Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague, ya ce ministocin harkokin waje na kungiyar ta G8 sun amince cewar dukanin kasashen da suka sa hannu a 'yarjejeniyar Geneva na da alhakin gurfanar da mutanen da ake zargin sun aikata fyaden.

Ya bayyana fyade a lokacin tashe tashen hankula a matsayin daya daga cikin rashin adalcin da ake ta tabkawa wanda ke haddasa wahalhalu masu yawa.

Mr Hague ya ce kungiyar ta G8 za ta bayar da dala miliyan 35 domin yaki da matsalar.

A halin da ake ciki kuma, Ministar harkokin mata ta Najeriya ta yi kiran da a rika yanke hukuncin kisa akan duk wanda aka samu da laifin aikata fyade.

Hajiya Zainab Maina ta ce, yanzu aikata fyade na karuwa sosai, kuma lamarin yana neman zama ruwan dare.

Ministar ta kuma yi kiran a kafa sashe na musamman a dukkan ofisoshin 'yan sanda dake Najeriya da za su rika kula da batun na fyade.

Karin bayani